Chelsea ta kare matakin kashe makudan kudade akan Torres

torres Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Torres ya barar da kwallo a wasanshi na farko a Chelsea

Darektan kula da wasanni a Chelsea Frank Arnesen ya kare matakin siyo Fernando Torres akan makudan kudade,inda yace kulob din bai daina rainon matasan 'yan kwallo ba.

Torres dan Spain mai shekaru 26 ya bar Liverpool ne akan pan miliyan hamsin a ranar 31 ga watan Junairu, rana guda da Chelsea ta bada Daniel Sturridge na wucin gadi zuwa Bolton.

Arnesen wanda shine shugaban karamar kungiyar Chelsea, ya shaidawa BBC cewar sunyi murnar siyo Torres.

Ana sukar Chelsea akan kashe makudan kudade wajen siyo 'yan kwallo a maimakon renon matasa ta karamar kungiyarta.

A cewar Arnesen mai kungiyar Chelsea Roman Abramovich yanason a siyo zaratan 'yan kwallo wanda suka goge don su lashe gasa daban daban.