David Beckham zai kara makwanni biyu a Spurs

beckham Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Beckham

Tsohon kaptin din Ingila David Beckham zai cigaba da horo tare da Tottenham na karin makwanni biyu a nan gaba.

Dan kwallon Los Angeles Galaxy ya koma Spurs na wucin gadi ne bayan kamalla kakar wasa ta bara a Amurka, don ya cigaba da kasancewa cikin koshin lafiya.

Tottenham a wata sanarwa ta ce"David Beckham zai cigaba da horo a kulob din zuwa 22 ga watan Fabarairu".

A don haka tsohon dan kwallon Ingilan zai koma LA Galaxy a ranar 24 ga wannan watan.

Kwangilar Beckham zata karke a watan Nuwamba a Amurka,kuma kocin Spurs Harry Redknapp ya ce watakila ya dauki hayar Beckham na dundundun.

Dan kwallon mai shekaru talatin da biyar, ya bugawa Ingila wasa a karawa 115.