FORMULA 1: Robert Kubica ya farfado

FORMULA 1: Robert Kubica ya farfado Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Likitoci sun ce Kubica ya taka wani mahimmin mataki

Dan wasan dake tuka motar kamfanin Renault Robert Kubica, ya farfado a daidai lokacin da ya fara murmurewa daga tiyatar da aka yi masa ta sa'o'i bakwai.

Kusan baki dayan hannun dan wasan mai shekaru 26 ya lalace, sannan ya samu karaya a kafada da kuma hannu a gasar FORMULA 1 da aka gudanar a Italiya ranar Lahadi.

"Likitoci sun ce ya taka wani mahimmin mataki," a cewar wakilinsa Daniele Morelli.

Wata sanarwa da kamfanin Renault ya fitar ta ce Kubica ya samu damar motsa 'yan yatsunsa kuma ya yi magana 'yan uwansa.

"Likitoci sun daga shi na wani dan lokaci," a cewar sanarwar ta Renault.