Frank Lampard na Chelsea zai rataya kaptin din Ingila

lampard
Image caption Frank Lampard

An nada Frank Lampard na Chelsea a matsayin kaptin din Ingila a wasanta da Denmark na ranar Laraba.

Lampard mai shekaru 32 zai ratayan kambum ne saboda kaptin na asali Rio Ferdinand da mataimakinshi Steven Gerrard sun samu raunin a wasannin da suka bugawa kulob dinsu a karshen mako.

Kocin Ingila Fabio Capello ya kuma bayyana cewar dan kwallon Arsenal Jack Wilshere zai buga tsakiya tare da Lampard.

Lampard wanda zai zama kaptin din Ingila a karon farko ya ce "Na yi matukar murna saboda ban zaci haka ba ".

Lampard ya bugawa Ingila wasa a fafatawa 83 inda ya zira kwallaye ashirin, kuma tun watan Agustan bara rabon daya bugawa Ingila kwallo saboda rauni.

Capello yace wasan zai sashi ya kara gane karfin tawagarshi kafin wasan da zasu kara da Wales a wata mai zuwa na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Turai.