Diego Milito na Inter zai yi jinya ta makwanni shida

milito
Image caption Michel Platini da Diego Milito

Dan kwallon Inter Milan da Argentina Diego Milito zai shafe makwanni shida yana jinya saboda a rauni a kafadarshi.

Sanarwar da Inter ta fitar ta ce wannan ne karo na biyar da Milito ya jimu.

Hakan na nufin cewar Inter zata fafata da Bayern Munich a zagayen gabda na kusada karshe na gasar cin kofin zakarun Turai da 'yan kwallon gaba guda biyu kacal wato Samuel Eto'o da Goran Pandev.

Kocin Inter Leonardo ya baiwa Milito kwarin gwiwa" Diego nada muhammancin gaske a wajenmu, don haka kada ya damu kanshi,ya maida hankali wajen murmurewa kawai".

A kakar wasan data wuce Milito mai shekaru 31 ya zira kwallaye da dama wajen taimakawa Inter ta lashe kofina uku a gasar daban daban.