Kamfanin Rasha na tattaunawa akan sayen Portsmouth

portsmouth
Image caption Portsmouth ta koma gasar Champoinship

Kungiyar Portsmouth ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da kamfanin wasu mutannen Rasha wato Convers Sport Initiative (CSI) wanda keda muradin siyan kulob din.

Kamfanin CSI nada hannu a kulob din Ferrari Russia da kuma tawagar kwallon gora na Spartak Moscow.

Daya daga cikin masu kamfanin CSI Chris Akers ya bayyana cewar: "Mun tattauna da kulob daban daban, hadda Portsmouth.

Shugaban CSI Vladimir Antonov a wasikar daya aikewa Portsmouth yace "Idan har muka sayi kulob din zamu maida hankali tare da saka kudade don ciyar da kulob din gaba".

Magoya bayan Portsmouth sun yi murnar wannan labarin musamman gannin cewar tun lokacin da dan Hong Kong Balram Chainrai ya sayi kulob din a shekara ta 2009 bai taka rawar da suka so gani ba.

Ana ganin cewar Balram Chainrai ya saka pan miliyan goma sha biyu a kulob din, amma ya bayyana cewar bai dace da cigaba da jan ragamar kulob din na lokaci mai tsawo.