Real Madrid zata gina cibiyar 'yan kwallo a Saudi Arabiya

perez
Image caption Shugaban Real Florentino Perez

Real Madrid ta kamalla yarjejeniya da gidauniyar Yarima Salman a Saudi Arabiya don gina cibiyar horadda matasan 'yan kwallo wato sports academy .

Shugaban Madrid Florentino Perez ya ce cibiyar 'yan kwallon zata dauki yara 'yan kwallo dari uku,kuma nada nufin kara dankon zumuncin tsakanin kulob din da kasar dake yankin gabas ta tsakiya.

Kungiyoyin Arsenal da Inter Milan tuni suka gina cibiyar horadda yara a fannin kwallon kafa a yankin gabas ta tsakiya.

Real Madrid na daga cikin kungiyoyin kwallon kafa a duniya masu arziki kuma Real din ta ce tanada cibiyoyin horadda 'yan kwallo 68 a kasashe 32.