Kyautar Laureus: Spain ce ta daya a 2010

Kyautar Laureus: Spain ce ta daya a 2010
Image caption Spain ta lashe gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a karon farko a tarihinta

An zabi tawagar Spain a matsayin kungiyar da ta fi kowacce taka leda a fagen wasanni a shekara ta 2010, a bikin bada kyautuka na Laureus da aka gudanar a birnin Abu Dhabi.

Spain, wacce ake wa lakabi da La Furia Roja, ta lashe gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a karon farko a tarihinta.

Spain ta doke Inter Milan wajen samun kyautar, duk da cewa Inter ta lashe gasar Serie A da Coppa Italia da kuma gasar zakarun Turai.

Har ila yau an kuma baiwa tsohon dan wasan Faransa Zinedine Zidane lambar yabo kan nasarorin da ya samu a rayuwarsa.

Daga cikin nasarorin da Zinedine Zidane ya samu a tarihinsa sun hada da lashe kofin kasashen nahiyar Turai da na zakarun Turai da kuma gasar cin kofin duniya.