Black Stars ta haskaka a wasan Goran Stevanovic na farko

stevanovic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Goran Stevanovic

Tawagar Black Stars ta Ghana ta baiwa sabon kocinta Goran Stevanovic nasara a karawar farko daya jagoranta inda ta doke Togo daci hudu da daya a wasan sada zumuncin da suka buga a Belgium.

Dominic Adiyiah ne ya fara ciwa Ghana tun kafin a tafi hutun rabin lokaci sannan Togo ta farke minti uku bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Jonathan Mensah da Samuel Inkoom ne suka ciwa Ghana sauran kwallaye biyun.

Wannan ne wasan farko da Stevanovic ya jagoranci Black Stars tunda aka na dashi a watan Junairu.

Kasashen biyu sun buga wasanne don shirye shiryen wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Afrika na shekara ta 2012.

A daya wasan da aka buga kuwa Ivory Coast ta casa Mali daci daya me ban haushi.

Wannan wasanne na farko da Didier Drogba ya bugawa Ivory Coast tun bayan gasar cin kofin duniya a bara a Afrika ta Kudu.