CAF ta daga wasu daga cikin karawar karshen wannan makon

caf
Image caption Tambarin CAF

Hukumar dake kula kwallon kafa a Afrika wato Caf ta dage wasu daga cikin karawar da yakamata ayi a karshen mako.

Fafatawar da aka daga ya shafi kungiyoyin da suke da akalla 'yan wasa uku dake fafatawa a gasar cin kofin kasashen nahiyar na 'yan kwallon cikin gida.

Karawa tara aka daga a gasar zakarun Afrika da kuma shida a gasar cin kofin Confederation.

Sanarwar da Caf ta fitar ta ce" za a buga wasannin ne a karshen makon watan Fabarairu.

Karawar da aka daga:

Gasar zakarun kwallon Afrika

JC Abidjan (CIV) v ASFAN (NIG)

Astres Douala (CMR) v US Bitam (GAB)

Djoliba (MLI) v East End Lions (SLE)

Cansado (MTN) v ASEC Mimosas (CIV)

Club Africain (TUN) v. APR (RWA)

Aduana Stars (GHA) v Wydad Casablanca (MAR)

Cotonsport Garoua (CMR) v Vital'O (BDI)

Vita Club (COD) v Ocean View (ZAN)

Zamalek (EGY) v Ulinzi Stars (KEN)

Gasar cin kofin Confederation:

AS Real (MLI) v Tevragh Zeina (MTN)

Sahel (NIG) v Dynamic (TOG)

AshantiGold (GHA) v Sewe San Pedro (CIV)

Africa Sport (CIV) v Sequence (GUI)

Inter Stars (BDI) v Missile (GAB)

DC Motema Pembe (COD) v KMKM (ZAN)