Chelsea da Liverpool sun 'kuskure' akan Gomez

gomez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mario Gomez

BBC ta fahimci cewar Bayern Munich taki amincewa da tayi akan Mario Gomez daga wajen Chelsea da Liverpool.

Liverpool da Chelsea sun yi zawarcin dan kwallon Jamus din amma sai aka ki yarda da tayin da suka bayar.

Gomez mai shekaru 25 ya koma Bayern ne daga Stuttgart akan kusan pan miliyan talatin, kuma a yanzu shine dan kwallon da yafi kowanne zira kwallo a Jamus kawo yanzu.

Chelsea ta kara karfin gabanta inda ta sayi dan Livepool Fernando Torres akan pan miliyan hamsin.

A yayinda ita kuma Liverpool ta sayi Andy Carroll da Luiz Suarez akan pan miliyan hamsin da takwas.

Yarjejeniyar Mario Gomez da Bayern zata karke ne a shekara ta 2013 kuma yana cikin tawagar 'yan Jamus data buga gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010.