Obafemi Martins ya samu izinin fara taka leda a Birmingham

obafemi
Image caption Martins Obafemi

Dan kwallon Najeriya Obafemi Martins ya koma Ingila bayan da aka bashi takardar izinin shiga kasar don ya takawa Birmingham City leda.

Ya hade da Birmingham a matsayin aro ne daga kungiyar Rubin Kazan ta Rasha a ranar 31 ga watan Junairu, amma rashin takardar izini ya hana shi fara buga kwallo.

Sanarwar da City ta fitar tace Martins mai shekaru 26 nada izinin buga wasa tsakaninsu da Stoke City a ranar Asabar.

Martins ya baya ya zira kwallaye 28 cikin karawa 88 daya bugawa Newcastle United daga shekara ta 2006 zuwa 2009.

Kocin Birmingham Alex McLeish na tunanin magoya bayan kulob din zasu yi murnar zuwan sabon dan kwallon.

Dan kwallon Najeriya din ya taba bugawa Inter Milan da Wolfsburg kwallo.