Emmanuel Adebayor ya jinjinawa Jose Mourinho

adebayor Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan kwallon Real Madrid na murnar kwallon Adebayor

Dan Togo Emmanuel Adebayor ya jinjinawa kocinsa Jose Mourinho akan cewar ya canza mashi dabarar wasa tun zuwanshi Real Madrid na wucin gadi.

Dan kwallon Manchester City din ya koma Madrid ne a watan gaya gabata a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Real nada damar sayen dan kwallon mai shekaru ashirin da shida na dun dun dun.

Adebayor wanda ya sha benci a City, a halin yanzu har ya zira kwallaye biyu a Real Madrid a wasaninta da Sevilla da kuma Real Sociedad.

Yace"Akwai saukin aiki tare da Mourinho, kwararre ne kuma ya habbaka mani wasa na".

Real Madrid a yanzu tana bayan Barcelona da maki bakwai akan tebur na gasar La Liga.