Real Madrid ce tafi arziki tsakanin kulob kulob na duniya

real
Image caption 'Yan kwallon Real Madrid

Kamfanin kwararrun akantoci mai suna Deloitte ya bayyana Real Madrid a matsayin kulob din daya fi kowanne arziki a duniya wato shekara shida kenan a jere.

Kidaddigar da kamfannin ya fitar bisa la'akari da kakar wasa ta 2009 zuwa 2010, ya ce harajin da manyan kulob ashirin suka samu ya haura Euro biliyan hudu.

Real ce ta farko a yayinda abokiyar hammayarta Barcelona ta cigaba da rike matakin na biyu sai Manchester United a matakin na uku.

Manchester City kuwa itace ta fi kowacce kungiya yinkurowa saboda daga matakin na ashirin ta koma na goma sha daya.

Arsenal da Chelsea da Liverpool sune na biyar dana shida dana bakwai.

Daga cikin kulob ashirin dake teburin na Deloitte, kulob bakwai daga Ingila suke.

Bugu da kari duka kulob din 20 mafi arziki a manyan gasar kasashen Turai suke wato Jamus da Italiya da Ingila da Spain da kuma Faransa.

* 1. Real Madrid: 438.6m euros * 2. Barcelona: 398.1m euros * 3. Man Utd: 349.8m euros * 4. Bayern Munich: 323m euros * 5. Arsenal: 274.1m euros * 6. Chelsea: 255.9m euros * 7. AC Milan: 235.8.m euros * 8. Liverpool: 225.3m euros * 9. Inter Milan 224.8m euros * 10. Juventus: 205m euros