Newcastle United ta sayi dan Finland Shefki Kuqi

shefki Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shefki Kuqi

Kungiyar Newcastle United ta tabbatar da sayen Shefki Kuqi har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan kasar Finland Kuqi mai shekaru 34 baida kungiya tunda ya bar kulob din Swansea a watan daya gabata.

Zai kasance makwafin Andy Carroll na wucin gadi, bayanda Carroll din ya koma Liverpool akan pan miliyan talatin da biyar.

Newcastle ta kara shiga rudu bayan da Shola Ameobi ya samu karaya a wasansu da Fulham a farkon wannan watan.

Kocin Newcastle Alan Pardew yace "muna bukatar karin dan kwallo a gabanmu saboda mun rasa Shola da Shefki".

Haka zalika an yiwa Ameobi tiyata a ranar Laraba,kuma ana saran zai murmure bayan makwani shida.