Rugby Union: Peter Stringer ya shiga tawagar Ireland

Image caption An dai saka dan wasan ne saboda rashin tabbas kan Tomas O'Leary

An saka Peter Stringer a tawagar Jamhuriyar Ireland da za ta fafata da Faransa a gasar kasashe shida ta kwallon zaruzuga na (rugby), a ranar Lahadi.

An dai saka dan wasan ne saboda rashin tabbas kan Tomas O'Leary wanda ke fama da rashin lafiya.

"Ba mu fitar da rai a kan Tomas ba....amma za mu jira mu ga irin ci gaban da zai samu," a cewar kocin Ireland Paul McNaughton.

Idan kuma bai warke ba, to za mu fara wasan da Eoin Reddan yayin da Stringer zai zauna a benci.