Redknapp :Bale ba zai buga wasanmu da AC Milan ba

bale
Image caption Gareth Bale ya rikita 'yan Inter Milan

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce watakila dan kwallonshi Gareth Bale ba zai buga wasansu da AC Milan na zakarun Turai ba saboda rauni a bayanshi.

Bale dan asalin kasar Wales ya soma murmurewa, amma ana saran Rafael van der Vaart zai buga wasan bayan ya mumurewa daga rauni a kafarshi.

Redknapp yace"Gareth ya samu sauki, amma bana tunanin zai buga wasanmu na ranar Talata".

Kocin ya kara da cewar akwai shakku akan koshin lafiyar Peter Crouch wanda shima yake da matsalar irinta Bale.

Rashin Bale zai iya kawowa Tottenham cikas a yinkurinta na taka rawar gani a gasar zakarun Turai, ganin cewar Bale gwarzo ne kuma yana da kokari wajen tada hankalin abokan hammaya.

"Kunga Gareth a wasanmu da Inter Milan, ya fitinesu, na san ba zasu manta ba a San Siro,"in ji Redknapp.