Roberto Carlos zai bar Brazil ya koma Rasha

carlos
Image caption Roberto Carlos

Kungiyar Corinthians ta Brazil ta sanarda cewar Roberto Carlos zai barta ya koma wata kungiya a kasar Rasha.

Dan kwallon mai shekaru talatin da bakwai na shiga damuwa ne bayanda magoya bayan kulob din suka yita musu ihu sakamakon fiddasu da aka a gasar cin kofin kulob kulob na yankin kudancin Amurka.

Duk da cewar shugaban Corinthians Andres Sanches ya tabbatar kare lafiyar 'yan kwallon, amma dai Carlos wanda ya takawa Real Madrid leda a wasanni 370 cikin shekaru goma sha daya a filin Bernabeu.

Sanches yace"Mun bashi tabbaci, amma ya nuna bai gamsu ba".

Rahotanni daga Brazil na nuna cewar Carlos zai koma kungiyar Anzhi Makhachkala akan Euro miliyan biyar.

Carlos da Ronaldo sun sha kakkausar suka bayanda aka fidda Corinthians a gasar, inda magoya bayan kulob din suka jefi motar 'yan kwallon da duwatsu.