Obuh zai cigaba da jan ragamar Flying Eagles zuwa 2013

obuh
Image caption John Obuh

Kocin tawagar 'yan kwallon Najeriya 'yan kasada shekaru 20 wato Flying Eagles, Mr John Obuh ya sabunta yarjejeniyarshi da hukumar kwallon kasar wato NFF don cigaba da jan ragamar matasan na karin wasu shekaru biyu masu zuwa wato 2013.

Obuh yana aiki ne ba tare da wata kwangila tsakaninshi da NFF ba saboda bayanda da ya jagoranci Golden Eaglets suk samu kyautar azurfa a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2009, sai aka dagashi ya koma Flying Eagles ba tare da wata kwangila a rubuce ba.

A halin yanzu kuma tawagar Flying Eagles din tare da John Obuh suna kasar Libya don buga wasannin sada zumunci a ranar Litinin da kuma Laraba.

Haka zalika NFF din ta dauki harar wani dan kasar Jamus Manfred Bender don yayi aiki ta reda John Obuh wajen karawa 'yan wasan najeriya gogewa kafin a fara gasar cin kofin matasan Afrika a watan mai zuwa.