Kwallon dana ci City shine mafi kyau a tarihina-Rooney

rooney Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Wayne Rooney ya bar 'yan City da tunani

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney ya ce kwallon daya zira a fafatawarsu da Manchester City shine yafi kowanne kayatarwa a kwallayen daya ci a tarihin kwallonshi kawo yanzu.

Nani ne ya bashi kwallo, shi kuma Rooney ya daga kafa kamar zai yi kwambe ya cilla ta a raga, inda aka tashi wasa Manchester United nada ci biyu Manchester City nada ci daya.

Sakamakon sauran karawar na gasar premiership:

*Arsenal 2 - 0 Wolverhampton *Birmingham City 1 - 0 Stoke City *Blackburn Rovers 0 - 0 Newcastle United *Blackpool 1 - 1 Aston Villa *Liverpool 1 - 1 Wigan Athletic *West Brom 3 - 3 West Ham United *Sunderland 1 - 2 Tottenham Hotspur