Osasuna ta kori kocinta Jose Antonio Camacho

camacho Hakkin mallakar hoto g
Image caption Jose Antonio Camacho

Kungiyar Osasuna ta Spain ta kori mai horadda 'yan kwallonta Jose Antonio Camacho.

Matakin kungiyar ya biyo bayan lallasata da Real Sociedad ta yi daci daya da nema a karshen mako.

Sanarwar da Osasuna ta fitar ta ce "Jose Antonio Camacho daga yanzu ba shi bane kocin Osasuna, mukamin da yake rike dashi tun ranar 14 ga Oktoban 2008".

Osasuna ta ce nan bada jimawa ba zata sanarda sunan wanda zai maye gurbin Camacho.

A halin yanzu dai Osasuna ce ta uku daga kasan teburin gasar La Liga, inda ta dara Malaga wacce ke can karshe da maki uku.