Dan Brazil Ronaldo ya yi ritaya daga tamaula

ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ronaldo Luiz Nazario de Lima

Dan kwallon Brazil Ronaldo wato dan kwallon da yafi kowanne cin kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya kuma gwarzon dan kwallon duniya sau uku, ya tabbatar da yin ritaya daga kwallo yana da shekaru talatin da hudu.

Dan kwallon Corinthians wanda ya fashe da kuka a taron manema labarai da ya kira, ya ce rashin koshin lafiya ne yasa shi daukar matakin, duk da cewar ruhinshi na son murza leda.

Ya ce "Zan bar kwallo, saboda a shekaru biyu da suka wuce na yita fama da rauni a kafafuwa na biyu, kuma abinda yasa zan yi haka kenan".

A shekaru goma sha hudun da ya shafe yana taka leda a Turai, Ronaldo ya ci kwallaye a PSV Eindhoven da Barcelona da Inter Milan da Real Madrid da kuma Ac Milan kafin ya koma Brazil a shekara ta 2008.

Ya lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2002 da Brazil, sannan ya kasance dan kwallon dayafi kowanne cin kwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya inda yaci kwallaye goma sha biyar a Jamus a shekara ta 2006.

Sau biyu ana bashi kambum gwarzon dan kwallon Turai wato a shekarar 1997 da kuma 2002, a yayinda ya bugawa Brazil wasa a karawa 97 inda ya zira kwallaye 62.