Ronaldo na Brazil ya yiwa kwallon kafa adabo

ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ronaldo

Tsohon gwarzon dan kwallon duniya Ronaldo Nazario na Brazil ya sanarda yin ritaya daga taka leda bayan ya shafe shekaru goma sha takwas ana damawa dashi.

Shahararen dan kwallon Brazil din ya samu nasarori a matakai daban daban a fagen kwallon kafa daga bangaren kasa zuwa kulob.

"O Fenomeno kamar yadda ake kiranshi, dan kwallo ne na gani na fada. Shine wanda yafi kowanne dan wasa zira kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya, inda yaci kwallaye goma sha biyar wato ya dara dan Jamus Gerd Muller da kwallo guda daya tal.

Ronaldo ya kasance daya daga cikin 'yan kwallo biyu a duniya da aka baiwa kyautar gwarzon dan kwallon duniya har sau uku, wato dashi da dan Faransa Zinedine Zidane.

'Yan kasar Brazil na daukar Ronaldo a matsayin gawurtaccen dan kwallo wanda ya shiga babban mataki a shafin tarihin kwallo Brazil, duk da cewar be kai hazikancin Pele a idon 'yan kasarba, amma dai yana tafiya kafada da kafada da irinsu Romario da Zico.

A tarihin yadda ya zira kwallaye dai, ya samu kyautuka da dama, amma kuma daga karshe sai ya yi karkon kifi.

Ronaldo ya shafe shekaru biyu a kungiyar Corinthians ta Brazil inda a shekara ta 2009 ake ta murna da kade-kade saboda zuwanshi da kuma nasarar da aka samu, sai dai daga karshe abin baiyi kyau ba, don a karke ne a tashin hankali.

'Ja-in-ja da Soke-Soke'

An saran shekara ta 2011 ta kasance shekarar da Ronaldo zai samu nasara, saboda burinshi shine ya taimakawa Corinthians ta lashe gasar kofin zakarun kasashen kudancin Amurka wato 'Copa Libertadores'.

Kungiyar Corinthians tana yankin Sao Paulo ne kuma tana daga cikin kulob kulob na Brazil masu farin jini da magoya baya "'yan gani kashe ni" fiye da miliyan ashirin da biyar. Amma duk da tarihin kulob din na lashe gasa daban daban, amma Corinthians bata taba lashe kofin Copa Libertadores ba.

Amma sai wannan burin ya janyo ja-in-ja da kuma tashin hankali.

A farko wannan watan, aka fidda Corinthians daga gasar inda kungiyar Deportes Tolima ta kasar Columbia ta samu galaba akanta.

Dubban magoya bayan kungiyar na ganin cewar Ronaldo ne ummul-aba-isin wannan rashin nasarar, kuma a washe gari a cikin filin horon Corinthians a Sao Paulo, sai magoya bayan suka yita mishi ihu suna kiranshi "O Gordo" wato Luti.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Da kyar Ronaldo ke gudu

Sannan bayan kwana guda kuma, magoya baya dari uku suka hadu a wajen filin horon kulob din suka jefi motar dake dauke da Ronaldo da sauran 'yan kwallo da duwatsu.

Sakamakon haka sai Ronaldo ya rubuta a shafinshi na Twitter cewar ya amsa laifin daya tafka a kashin da aka baiwa Corinthians, amma sai yayi Allah wadai da tashin hankalin. Ya kara da cewar yana tunanin yin ritaya.

A ranar Juma'ar data gabata ne wannan matsin lambar akan 'yan wasan Corinthians, yasa Roberto Carlos ya sanarda cewar zai koma taka leda a Rasha, inda yace ana yiwa iyalanshi barazana.

A ranar Lahadi, Ronaldo ya tabbatar da cewar zai yi ritaya daga kwallo. Hujjar daya bayar ita ce jikinshi ba zai iya daukar gurmuzu na kwallo ba,amma ruhinshi na bukatar tamaula.

'Soyayya'

Shekaru biyu da suka wuce ne, bayanda Ronaldo ya canza sheka daga AC Milan zuwa Corinthians, ya bayyana komawarshi kulob din a matsayin abune na soyayya.

An bayyana yarjejeniyar a Brazil a matsayin ta musamman a tarihin sauya sheka na 'yan kwallo, a yayinda wasu kuma ke sukar lamarin akan cewar dan kwallo ne wanda ya fara gajiya yake neman hanyar yin ritaya a mutunce.

'Ronaldo ya rufe bakin masu suka'.

A shekara ta 2009, ya ci kwallaye masu mahimmanci da suka taimakawa Corinthians ta lashe gasa biyu a Brazil wato gasar cin kofin kulob kulob na Sao Paulo da kuma Copa du Brazil, wato kofi na biyu mafi daraja a kasar.

Amma, can a karshen shekara lokacin gasar cin kofin kasar, yaji rauni abinda ya tilasta mashi daina taka leda har kashen kakar wasa.

Shekara ta 2010 ta kasance shekarar da aka saran za a samu nasarori, inda Corinthian ke fatar lashe gasar Libertadores, amma sai Ronaldo da sauran 'yan wasan suka kasa doke Flamengo a wasan kifa daya kwala.

Ritayarshi bata zowa mutane a matsayin bazata ba, saboda yana ta fama da rauni da kuma karin nauyi.

Image caption 'Yan wasan Corinthians na jinjinawa Ronaldo

Wasu masu sharhi sun dauka Ronaldo ba zai kara haskakawa ba a fagen tamaula lokacin da ya samu rauni a gwiwarshi a shekarar 1999, amma sai ya dawo da karfinshi , ya lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2002 da kuma kofin La Liga sau biyu tare da Real Madrid.

Wasu zasu tunashi saboda kwallaye biyun daya zira a wasan karshe na gasar cin kofin duniya tsakaninsu da Jamus a shekara ta 2002, a yayinda wasu zasu dunga tuna rashin taka rawar ganin da yayi a wasan da Faransa ta doke Brazil daci uku da nema a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 1998.

Amma dai tabbas da wuya a manta Ronaldo.