Dan kwallon Mali Mama Sidibe zai yi doguwar jinya

sidibe Hakkin mallakar hoto g
Image caption Mama Sidibe

Dan kwallon Stoke City Mama Sidibe ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda rauni a kafarshi a karo na biyu cikin watanni shida.

Dan kwallon Mali mai shekaru 31 yana gabda komawa taka leda sai ya samu sabon rauni a ranar Alhamis.

Kocinshi Tony Pulis ya tabbatar da raunin amma ya ce baida nasaba da raunin daya samu a wasansu da Tottenham Hotspur a watan Agustan bara.

Kocin yace"a idon sawun da yaji rauni, anan ya kara jimuwa". Ya kara da cewar "na san cewar yana da kwazo da sadaukar da kai, don haka zamu bashi dukannin goyon bayan da yake bukata".

Sidibe ya soma murmurewa kafin lamarin ya ta'azara.