Nasri ya warke don fafata wa da Barca

Samir Nasri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samir Nasri ya fi kowa zira kwallaye a Arsenal bana

Arsenal ta saka dan wasanta na tsakiya Samir Nasri a jerin wadanda za su fafata da Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai.

Dan wasan dai ya shafe makonni biyu yana fama da rauni.

Sai dai koci Arsene Wenger ya ce sai ranar Laraba ne zai yanke shawara ko za a fara wasan da Nasri ko kuma a'a.

Dan wasan tsakiya Abou Diaby ba zai samu damar buga wa ba saboda raunin da yake fama da shi, amma Tomas Rosicky ya dawo kuma zai taka leda.

Zakarun Spain Barcelona wadanda suka fitar da Arsenal a gasar ta bara, yawancin 'yan wasansu na nan lafiya kalau.