Zat Knight zai yi jinyar makwanni shida

Image caption Dan wasan mai shekaru 30 ya samu raunin ne a wasan da kungiyar ta lashe Everton da ci 2-0

Dan wasan Bolton Zat Knight zai yi jinyar makwanni hudu ko shida bayan da ya samu rauni a gwuiwarsa.

Dan wasan mai shekaru 30 wanda ke taka leda a baya ya samu raunin ne a wasan da kungiyar ta lashe Everton da ci 2-0.

"Abin bai yi muni kamar yadda muka zata da farko ba, amma zai hana shi taka leda na lokaci mai tsawo," a cewar manajan kungiyar Owen Coyle.

"A yanzu ta tabbata ba zai taka leda ba har tsawon makwanni hudu ko shida, wanda ba karamar asara ba ce."

Coyle ya kara da cewa: "Wannan mummunan labari ne ga Zat, saboda ya buga dukkan wasan da mu ka yi tunda na karbi ragamar al'amura kusan shekara guda kenan.