CAF:Najeriya za ta tura tawaga don Galadima ya maye gurbin Adamu

galadima Hakkin mallakar hoto b
Image caption Ibrahim Galadima

Najeriya za ta tura babbar tawaga zuwa taron koli na hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato CAF don nemawa Alhaji Ibrahim Galadima goyon bayan don a zabeshi a kwamitin zartarwar FIFA.

Tawagar karkashin ministan wasannin kasar Farfesa Taoheed Adedoja zata je Sudan don ganin cewar Galadima ya maye gurbin Amos Adamu wanda aka kora bisa zargin cin hanci da rashawa a watan Nuwamban bara.

Tawagar zata hada da shugaban NFF Alhaji Aminu Maigari da tsohon shugaban NFA Dominic Oneya da wasu jiga jigai a harkar kwallon kafa a Najeriya don gannin cewar Galadima ya samu nasara.

Ibrahim Galadima mai shekaru hamsin da tara, tsohon shugaban NFA ne kuma ya rike mukamai da dama a bangaren bunkasa kwallon kafa a Najeriya a matakai daban daban musaman a jihar Kano da matakin gwamnatin tarayya.

Farfesa Adedoja yace" wannan shiri ne na Najeriya, kuma ba zamu yi kasa a gwiwa ba, mun shirya tsaf don ganin cewar dan Najeriya ya cigaba da rike kujerar."