NFF na lura da 'yan Flying Eagles dake Libya

obuh
Image caption John Obuh

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Najeriya NFF ta ce tana lura da al'amura a Libya saboda tawagar 'yan kwallon kasar 'yan kasada shekaru ashirin sunje rangadi.

Flying Eagles a halin yanzu suna birnin Benghazi inda aka buga wasanin sada zumunci.

Amma zanga zangar kin jinin gwamnatin tasa 'yan Najeriyar cikin fargaba.

Ofishin jakadancin Najeriya a Libya ta shawarci 'yan kwallon kada su jefa kansu cikin yamusti.

Sanarwar da NFF ta fitar ta ce sun sa ido don lura da lamarin.

A ranar Laraba ake saran 'yan Najeriya din zasu bar Libya zuwa kasar Turkiya don cigaba da wasannin sada zumunci.