An jinjinawa Raul Gonzalez na Spain saboda kafa tarihi

raul Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Raul Gonzalez na Schalke 04

An jinaniwa dan kwallon Spain Raul Gonzalez saboda kafa tarihi a matsayin wanda yafi kowanne cin kwallaye a tarihin gasar kwallon Turai.

Yaci kwallaye saba'in da daya kawo yanzu inda ya shiga gaban Filippo Inzaghi wanda a baya yake kan gaba.

Christoph Metzelder na Schalke 04 ya ce "ya kafa tarihi, ina taya shi murna".

Raul ne ya farkewa Schalke 04 kwallo inda aka tashi kunen doki tsakaninta da Valencia a wasan gasar zakarun Turai na ranar Talata.

Kocin Schalke,Felix Magath yace "ba abun mamaki bane, saboda Raul gogaggen dan kwallo ne".

Raul ya lashe gasar cin kofin La Liga tare da Real Madrid da kuma gasar zakarun Turai uku inda ya zira kwallaye 323 a wasanni 741 a Bernabeu.

Dan kwallon mai shekaru talatin da uku ya fara take leda ne a Real Madrid a shekarar 1994-1995 a matsayin dan shekaru 17, ya bar Bernabeu a watan Yulin 2010 ya hade da Schalke.