Dan kwallon Liverpool Sterling na gabda kafa tarihi

sterling Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Raheem Sterling

Matashin dan kwallo Raheem Sterling zai iya zamowa dan wasa mafi karanci shekaru a tarihin Liverpool da zai buga mata kwallo inda har aka sakashi a fafatawa tsakaninsu da Sparta Prague na ranar Alhamis.

Sterling wanda zai cika shekaru goma sha shida a watan Disamba, an ji mamakin sakashi cikin tawagar 'yan kwallon da zasu buga wasan.

Sterling yaci kwallaye biyar a wasan da kulob din matasan Liverpool suka lallasa Sothend daci tara da nema.

Dan kwallon Ingilan da aka haifa a Jamaica, yana zuwa makarantar sakadare a Rainhill High School a Prescot, kuma yan haskakawa matuka tunda ya bar Queens Park Rangers ya koma Anfeild.

Sterling na daga cikin matasan da aka gayyata a tawadar ciki hadda John Flanagan, Conor Coady, Robinson da kuma Tom Ince.