Uefa:Gattuso zai fuskanci kwamitin da'a ranar Litinin

gatusso
Image caption Genarro Gattuso da Joe Jordan

Ana tuhumar dan kwallon AC Milan Gennaro Gattuso akan saba ka'idar wasanni, bayanda ya yiwa mataimakin kocin Tottenham Joe Jordan karon kai.

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Turai wato Uefa ta ce Gattuso zai fuskanci kwamitin da'a a ranar Litinin mai zuwa don ya kare kanshi.

Dokar da'ar Uefa ta gindaye dakatarwa ta akalla wasa guda ga duk wanda ya nuna halayyar da suka sabawa ka'idojinta.

Amma hukuncin zagin dan wasa ko kuma wani a lokacin wasa, za a dakatar da mutum na wasanni uku ko fiye da haka.

Gattuso ya yiwa Jordan karon kai a wasan da AC Milan ta sha kashi daci daya me banhaushi a filinta na San Siro a zagaye na biyu na gasar zakatun Turai a ranar Talata.

Dan kwallon Italiyan ya yi nadama kuma ya numi afuwa akan abinda yayi.