Hicks da Gillet zasu iya samun diyya akan Liverpool

hicks
Image caption Tom Hicks da George Gillet

Dan Amurka Tom Hicks wato tsohon mai kungiyar Liverpool ya samu nasara a kotu a yinkurinshi na samun diyya saboda sayarda kulob din ga kungiyar baseball ta Boston Red Sox.

Hicks da George Gillett sun sha alwashin yin amfani da hanyoyin shari'a don samun diyyar dala biliyan daya da rabi akan sayarda Liverpool akan pan miliyan dari uku.

Hicks da Gillett sun bayyana cinikin a matsayin haramtacce amma sai aka siyarda kulob din bisa goyon bayan Banki Scotland wanda ke bin Liverpool bashi.

Hicks da Gillett sun ce sunyi tayin biyan basukan na bankin Scotland din amma sai aka ki amince da shi.