'Chelsea ta yi taka tsantsan'- Lampard

Hakkin mallakar hoto b

Dan wasan Chelsea Frank Lampard ya ce zai zama gaggarumin koma baya ga kungiyar muddin kungiyar bata samu tsallakewa domin taka leda a gasar zakarun Turai na badi ba.

Chelsea dai ta buga canjaras a wasan da ta fafata da Fulham a gasar Premier a ranar litinin, abun da kuma ya sa ta koma matsayi na biyar a gasar.

Chelsea dai na bayan mai jagoranci gasar ta Premier wato Manchester United da maki goma sha biyu, a yayinda dan wasan ya ke karyata rahotannin dake nuni da cewa sun fidda rai a gasar ta Premier.

Lampard ya ce dolene kungiyar ta zage damtse domin shiga cikin rukunin kungiyoyi hudu a gasar da za su cancanci taka leda a gasar ta zakarun Turai ta badi.