Nafi son mu lashe gasar Turai akan na premier-Lampard

lapard Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Frank Lampard

Dan kwallon Chelsea Frank Lampard ya bayyana cewar zai iya barin batun neman lashe gasar premier domin su lashe gasar zakarun Turai.

Chelsea dai bata taba lashe gasar zakarun Turai ba a tarihinta, amma a shekara ta 2008 ta kuskure a wasan karshe inda Manchester United ta doke ta a bugun penariti.

Lampard ya shaidawa jaridar The Mirror cewar "bana son fifita wata gasa akan wata, amma tun na lashe gasar premier sau uku, a yanzu nafi son lashe gasar zakarun Turai".

Dan kwallon mai shekaru talatin da biyu ya ce irin rawar da suke takawa a Turai zai basu kwarin gwiwa ganin cewar suna fuskantar matsaloli a gasar premier ta Ingila.

Lampard ya kara da cewar"ya dangata da tawagar, idan muna kwazo a Turai, ina zai taimaka mana a Ingila".