Za a dinga kallon gasar cin kofin duniya kyauta a Birtaniya

kofi
Image caption Kofin gasar kwallon duniya

Wata babbar kotun nahiyar Turai-EGC ta yanke hukuncin cewar masu kallon kwallo a yankin Birtaniya zasu kalli manyan gasar kwallon kafa na duniya kyauta a gidajen talabijin.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa da kuma Uefa sun kalubalanci hukuncin da gwamnatin Birtaniya ta yanke akan cewar gasar cin kofin duniya da kuma na zakarun Turai da kofin Uefa za a kallesu a kyauta.

Birtaniya ta saka wadannan gasannin a matsayin bukukuwan wasanni masu mahimanci wadanda aka kare su.

Kotun ta ce a yanzu mambobin kungiyar tarrayyar Turai wato EU zasu iya haramta watsa wadannan gasannin a tasoshin talabijin da ake biya.

Kotun kuma tayi watsi da matakin Fifa akan Belgium saboda nuna wasannin gasar cin kofin duniya a tashoshin talabijin da ba a biya a kasar.

Fifa da Uefa sun bayyana cewar wannan matakin zai kawo katsalanda a wajen sayarda hakkin mallakar nuna wasanni a farashin me tsoka.

Hukumomin biyu sun ce babu hujjar nuna irin wadannan gasar a kyauta a gidajen talabijin na Birtaniya.