Giggs ya sabonta yarjejeniya da Manchester United

Kwarren dan wasan Wales Ryan Giggs ya sabonta kwantaraginsa da kungiyarsa ta Manchester United na tsawon shekara guda.

Hakan na nufin cewa dan wasan mai shekarun haihuwa 37 zai kai tsawon shekaru 21 daya a kungiyar da ya fara taka mata leda tun a shekarar 1991.

Dan wasan ya takawa United leda a wasanni 24 a kakkar wasan bana.

Ya ce; "ina matukar farin ciki kan irin gudunmuwar da nake ba kungiyar, kuma ina da kwarin gwiwa zan ci gaba da hakan".