Frank Arnesen zai bar Chelsea ya koma Hamburg

 Frank Arnesen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Frank Arnesen

Darektan kula da wasanni a kulob din Chelsea Frank Arnesen ya kulla yarjejeniya ta shekaru uku don rike irin mukamin a kulob din Hamburg ta Jamus.

Dan shekaru hamsin da hudu, wanda a baya ya rike irin mukamin a Tottenham, ya sanarwa a bara cewar zai bar Chelsea a karshen kakar wasa mai zuwa.

Arsensen yace"bani da shakku cewar yadda muke da karfi zamu yanke hukunci yadda ya dace"

Lee Congerton wanda ke zakulowa Chelsea matasan 'yan kwallo shima zai koma Jamus.

Hamburg ta baiwa Arnesen matsayinne bayan da darektan kula tsare tsare na kwallon Jamus Matthias Sammer yace baison mukamin.

Shugaban Hamburg Ernst-Otto Rieckhoff yace siyo Arnesen zai magance matsalar rashin darektan wasanni na shekaru biyu.

A shekara ta 2004 ne Arnesen ya koma Spurs kafin ya koma Chelsea bayan shekara guda.