An tsawalla farashen tikitin wasan karshe na gasar zakarun Turai

ferguson
Image caption Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce farashin tikitin wasan karshe na gasar zakarun Turai da za a buga a filin Wembley abun taikaici ne.

Farashin tikiti mafi karanci don kallon wasan a ranar 28 ga watan Mayu za a biya pan 176.

Amma dai magoya bayan kulob din biyu da zasu buga wasan zasu biya pan tamanin.

Ferguson ya ce"wannan lamarin yayi tsakani, kai abun kunya ne da taikaci, gashi babu abinda zamu iya yi akai".

Hukumar kwallon kafa ta Turai-Uefa a ranar Alhamis ta sanarda cewar tikiti dubu goma sha daya ne za a sayarwa 'yan kallo don wasan karshen.

Farashin tikitin 'yan kallon da basa goyon bayan kowacce kungiya ya soma ne daga pan 176 zuwa pan 326.

An ware tikiti dubu hamsin ga magoya bayan kulob din biyu da zasu buga wasan karshen daga cikin wajen zama dubu tamanin da shida a filin Wembley.