'Ba zan bar Chelsea ba'- Ancelotti

Image caption Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce babu abun da zai sa ya bar Chelsea duk da cewa an fidda kungiyar a gasar cin kofin FA.

Everton dai ta fidda Chelsea a filin Stamford Bridge a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan sun tashi daya da daya a cikin lokaci.

Wannan dai na nuna alamun cewar Chelsea ba ta da rabon lashe gasa ko guda a bana.

Ancelotti dai ya ce baya tunanin ajiye aikin shi duk da rashin nasarar da kungiyar ta ke fuskanta a kakar wasan bana.

"Bani da ikon barin aiki da kashin kaina, sai mai kungiyar ya zartar da abun da ya ke so". In ji Ancelotti.