Uefa ta dage Gennaro Gattuso daga buga wasanni hudu

gattuso
Image caption Gennaro Gattuso ya makure Joe Jordan

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Turai-Uefa ta dakatar da dan kwallon AC Milan Gennaro Gattuso na wasanni hudu saboda karon kai da ya yiwa mataimakin kocin Tottenham Joe Jordan.

Kwamitin da'a na Uefa a ranar Litinin ya yanke hukuncin cewar Gattuso yaci zarafin Joe Jordan a wasan gasar zakarun Turai da aka doke AC Milan.

Uefa ta tuhumi Gattuso akan saba ka'idar wasanni kuma zai shafe wa'adin daina duk wata gasa da Uefa ta shirya guda hudu a jere.

Gattuso nada kwanaki uku na daukaka kara idan yana da bukatar yin hakan.

Gattuso ya yi nadamar aikata wannan laifin inda ya nemi afuwa.

Gattuso yace "na amsa laifin abinda ya auku tsakani na da Jordan".