Bani da muradin Jack Wilshere a Barcelona-Guardiola

pep
Image caption Pep Guardiola

Kocin Barcelona Pep Guardiola ya ce baida bukatar sayen matashin dan kwallon Arsenal Jack Wilshere duk da cewar dan wasan ya haskaka a karawarsu ta ranar Laraba a gasar zakarun Turai.

Dan kwallon mai shekaru goma sha tara, a bashi kyautar dan wasa mafi bajinta a fafatawar, kuma tuni aka fara alakantashi da Barca saboda irin salon wasanshi.

Guardiola ya jinjinawa Wilshere amma amma dai ya ce baya tunanin siyo matashin dan wasan, sannan ya kara da cewar Barcelona ba zata sayi kowa ba a Emirates ciki hadda Cesc Fabregas.

Yace"Wilshere babban dan wasa ne na Arsenal kuma bana tunanin Arsene Wenger zai sayarda goggaggun 'yan kwallonshi".

Guardiola ya kara da cewar "arsenal bangare ne me kyau,suna da babban koci".