Za a ragewa kungiyar Plymouth Argyle maki goma

plymouth
Image caption Plymouth Argyle

Za a ragewa kungiyar Plymouth Argyle maki goma saboda bada sanarwar niyyar nada kantoma don lura da ita ba.

Kungiyar dake taka leda a League One na fama da matsalolin kudaden da kuma batun haraji a kakar wasa ta bana.

Sanarwar da Kulob din ta fitar ta ce"matakin kulob din shine don ya kare kanshi daga durkushewa daga masu bada bashi".

Sanarwar ta kara da cewar"hakan ba yanan nufin cewar kulob din ya durkushe ko kuma yana gabda durkushewa".

Wannan matakin zai maida kulob din kasan tebur da maki ashirin da uku.

An nada David Hinchliffe wanda ke aiki da lauyoyin Walker Morris Solicitors a matsayin kantoma wanda zai yi aiki tare da dan kwamitin gudanarwar Plymouth Peter Ridsdale.