Chelsea na nan daran-da-kau - Ancelotti

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Everton ce ta doke Chelsea a gasar FA

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce kungiyar na nan daran-da-kau, kuma za ta iya taka rawa sosai duk da matsalolin da take fuskanta.

Gasar zakarun Turai ita ce kawai ake ganin Chelsea na da damar lashewa a bana bayan da aka fitar da ita daga gasar FA, kuma take mataki na biyar a gasar Premier.

"Kakar bana za ta iya kasancewa mafi kyau a gare mu. Za kuma ta iya kasancewa mafi muni. Bani da tabbas," a cewar Ancelotti.

"Amma ku jira ku gani, Chelsea bata mutu ba. Chelsea na nan daran."

Chelsea za ta kara da FC Copenhagen a gasar zakarun Turai a ranar Talata, inda mai kungiyar Roman Abramovich ke neman lashe gasar a karon farko tun lokacin da ya sayi kulob din a shekara ta 2003.