Anelka ya taimakawa Chelsea

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Chelsea ta dade tana fuskantar matsala

Chelsea ta saukaka matsin lambar da ke kan koci Carlo Ancelotti bayan da ta doke FC Copenhagen da ci 2-0 a gasar zakarun Turai.

Nicolas Anelka ne ya fara zira kwalllon farko bayan da tsohon dan wasan Chelsea Jesper Gronkjae ya yi kuskure.

Chelsea ta kara tazarar ta a wasan bayan da Frank Lampard ya taimakawa Anelka inda ya zira kwallo ta biyu.

Tawagar ta Ancelotti ta mamaye wasan, sai dai sabon dan wasa Fernando Torres bai zira kwallo ba.

Wannan nasar ta saukaka matsin lambar da ke kan Carlo Ancelotti bayan da aka fitar da Chelsea daga gasar cin kofin FA a karshen mako.