FIFA:Galadima na takara da mutane hudu

galadima Hakkin mallakar hoto b
Image caption Ibrahim Galadima

Dan Najeriya Alhaji Ibrahim Galadima na daga cikin mutane biyar dake takarar gurbin kujeru biyu a kwamitin gudanarwar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA wanda aka kebewa nahiyar Afrika.

A ranar Laraba ne za ayi zaben neman kujeru biyu na Fifa a birnin Khartoum na Sudan, inda kuma za a zabi wasu wakilai shida a kwamitin gudanarwar hukumar kwallon Afrika wato CAF.

Galadima na takara ne da Danny Jordan na Afrika ta Kudu da Jacques Anouma na Ivory Coast da Mohamed Raouraoua na Algeriya da kuma Suketu Patel na kasar Seychelles.

Sai dai tsohon gwarzon dan kwallon Afrika kalusha Bwalya na Zambia ya janye daga takaran.

Anouma na neman wa'adi na biyu ne akan kujerar a yayinda Amos Adamu na Najeriya aka dakatar dashi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Masu nazari akan harkar wasanni na ganin cewar Danny Jordan na Afrika ta Kudu zai iya samun daya daga cikin guraben biyu ganin cewar ya taka rawar gani a shugabancin da yayi na jagorantar gasar cin kofin duniya a bara a karon farko a nahiyar Afrika.