Dan West Ham Keane zai shafe wata guda yana jinya

keane
Image caption Robbie Keane

Dan kwallon West Ham Robbie Keane zai shafe wata guda yana jinyar rauni a kafarshi.

Dan wasan mai shekaru talatin da haihuwa, ana shakkun ba zai buga wasan Ireland da Macedonia na share fagen na neman gurbin gasar cin kofin kasashen Turai a shekara ta 2012.

Keane wanda hammers ta siyo a matsayin aro daga Tottenham, bai buga wasan da West Ham ta lallasa Burnley daci biyar da daya a wasan gasar cin kofin FA.

Kafin a fara wasan, daya daga cikin masu horadda West Ham Wally Downes ya karyata rahotanni cewar Matthew Upson ba zai kara taka leda a kakar wasa ta bana saboda rauni.

Kungiyar ta ce kaptin dinta mai shekaru talatin da daya ana gwada lafiyarshi kuma watakila ya koma wasa a wata mai zuwa.