'Yan Man United biyar ba zasu kara da Marseile ba

united Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwarzayen Manchester United

Manchester United zata buga wasa tsakaninta da Marseile na gasar zakarun Turai ba tare da Anderson, Rio Ferdinand, Ryan Giggs, Jonny Evans da kuma Michael Owen a ranar Laraba.

Cikin 'yan kwallon, Anderson ne kadai ya buga wasa ranar Asabar inda United ta doke Crawley Town a gasar cin kofin FA.

Kaptin Ferdinand bai taka leda tun ranar biyar ga watan Fabarairu a wasansu da Wolves a yayinda shi kuma Evans ke fama da rauni a idon sawun shi.

Giggs da Owen na cikin tawagar data kara da Manchester City a ranar 12 ga watan Fabarairu.

Matsalar 'yan kwallon baya da United ke fama dashi, yasa watakila Chris Smalling ya buga tare da Nemanja Vidic.

Tawagar Manchester United: Van der Sar, Kuszczak, Lindegaard; Vidic, O'Shea, Brown, Rafael, Fabio, Evra, Smalling; Scholes, Gibson, Nani, Carrick, Fletcher, Bebe, Obertan, Tunnicliffe; Rooney, Berbatov, Hernandez, King.