Van Persie ba zai bugawa Arsenal a wasanta da Stoke ba

persie
Image caption Robin van Persie

'Yan kwallon Arsenal Robin van Persie da kuma Laurent Koscielny ba zasu buga wasan kulob din da Stoke City na ranar Laraba a gasar premiership ba.

An gano 'yan kwallon biyu suna fama da rauni, abinda zai iya hanasu buga wasan.

Sai dai kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce akwai yiwuwar 'yan kwallon biyu su murmure kafin wasa cin kofin Carling na ranar Lahadi.

Ita kuwa kungiyar Stoke zata duba lafiyar Matthew Etherington wanda ya jimu a wasansu da Brighton.