FIFA:Raouraoua ya kada Galadima da Jordan

fifa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan Algeriya Mohamed Raouraoua ya maye gurbin Amos Adamu na Najeriya

An zabi shugaban hukumar kwallon Algeriya Mohamed Raouraoua a kwamitin gudanarwar hukumar kwallon duniya Fifa.

Raouraoua ya samu gurbi daya daga cikin biyu a yayinda shugaban kwallon Ivory Coast Jacques Anouma ya samu zabe a karo na biyu

Raouraoua ya maye gurbin Amos Adamu na Najeriya wanda aka dakatar bisa zargin cin hanci da rashawa.

Raouraoua ya samu kuri'u 39 sai Anouma ya samu kuri'u 35 a yayinda Suketu Patel na kasar Seychelles ya samu kuri'u 12 sai Danny Jordan na Afrika ta Kudu mai kuri'u 10. Ibrahim Galadima na Najeriya kuwa ya samu kuri'u biyar kacal.

Wakilan hukumar kwallon kafa na Afrika wato Caf daga kasashe 53 a birnin Khartoum na Sudan inda kowace kasa keda kuri'u biyu.

Zaben a kwamitin gudanarwar Fifa:

Mohamed Raouraoua (Algeria) - 39 Jacques Anouma (Ivory Coast) - 35 Suketu Patel (Seychelles) - 12 Danny Jordann (afrika ta Kudu) - 10 Ibrahim Galadima (Najeriya) - 5