Golan City Given zai shafe watanni uku yana jinya

given
Image caption Shay Given

Golan Manchester City Shay Given zai shafe akalla watanni uku yana jinyar rauni a kafadarshi.

Dan shekaru talatin da hudun ya buga wasanni hudu kacal a kakar wasa ta bana, kuma zai ziyarci kwararren likita a ranar Laraba.

Kocin City Roberto Mancini yace" ya samu irin raunin daya samu a bara, ina tunanin yana bukatar tiyata".

Koda yake an cire daga tawagar Ireland na karawa da Macedonia a wasan neman gurbi a gasar cin kofin kasashen Turai, akwai yiwuwar Given ba zai kara bugawa kasarshi ko kulob dinshi kwallo ba.

Mancini ya kara da cewar "abun takaici ne a gere mu, mun rasa goggaggen dan kwallo".

A halin yanzu dai Joe Hart ne babban golan City kuma bisa dukkan alamu Shay Given ya kamawa kungiyar wasanshi na karshe.